Mika 5:5 - Littafi Mai Tsarki5 Zai zama salamarmu. Sa'ad da kuma Assuriyawa za su kawo mana yaƙi, Za su tattake kagaranmu, Za mu sa makiyaya bakwai da shugabanni takwas su yi gāba da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Zai kuma zama salamarsu. Sa’ad da Assuriyawa suka kawo wa ƙasarmu hari suka tattake kagarunmu, za mu tā da makiyaya bakwai, har ma shugabannin mutane takwas su yi gāba da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Akwai abu shida, i, har bakwai ma, waɗanda Ubangiji yake ƙi, waɗanda ba zai haƙura da su ba, duban raini, harshe mai faɗar ƙarya, hannuwan da suke kashe marasa laifi, kwanyar da take tunane-tunanen mugayen dabaru, mutum mai gaggawar aikata mugunta, mai yawan shaidar zur, mutum mai ta da fitina a tsakanin abokai.