Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mika 5:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Shi kuwa zai tashi ya ciyar da garkensa da ƙarfin Ubangiji, Da ɗaukakar sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuwa zauna lafiya, Gama zai zama mai girma cikin duniya duka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Zai tsaya yă yi kiwon garkensa da ƙarfin Ubangiji, cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa za tă kai har ƙarshen duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mika 5:4
37 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ka yi kiwon mutanenka da sandanka, Wato garken mallakarka, Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi A tsakiyar ƙasa mai albarka. Bari su yi kiwo cikin Bashan da Gileyad Kamar a kwanakin dā.


“Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda,


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.


Daga Yahuza bawan Yesu Almasihu, ɗan'uwan Yakubu zuwa ga kirayayyu, ƙaunatattun Allah Uba, keɓaɓɓu ga Yesu Almasihu.


Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu,


Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.”


Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uba na cikina, ni kuma ina cikin Uba.”


“Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.


Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.


“ ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, Domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, Wanda zai zama makiyayin jama'ata, Isra'ila.’ ”


Ubangiji ya ce, “Zan datse karusa daga Ifraimu, In datse ingarman yaƙi a Urushalima, Zan kuma karya bakan yaƙi. Sarkinki zai tabbatar wa al'umman duniya da salama, Mulkinsa zai zama daga teku zuwa teku, Daga Kogin Yufiretis zuwa matuƙar duniya.”


Ubangiji ya ce, “Bawana zai yi nasara a aikinsa, Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.


Ubangiji ya zaɓe ni tun kafin a haife ni. Ya maishe ni bawansa domin in komo da mutanensa, In komo da jama'ar Isra'ilan da aka warwatsar. Ubangiji ya ba ni daraja, Shi ne tushen ƙarfina.


Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka, Da kuma darajar ɗaukakar mulkinka.


Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama'ar Isra'ila, Da tabbatacciyar ƙauna da aminci. Dukan mutane ko'ina sun ga nasarar Allahnmu!


Ubangiji sarki ne! Yana saye da ɗaukaka, suturarsa ƙarfi ne. Hakika duniya ta kahu sosai a inda take, Ba kuwa za ta jijjigu ba.


Ku yabi sunansa mai daraja har abada, Allah ya sa ɗaukakarsa ta cika dukan duniya! Amin! Amin!


Mulkinsa ya kai daga teku zuwa teku, Daga Kogin Yufiretis, har zuwa iyakar duniya.


Dukan al'ummai za su tuna da Ubangiji, Za su zo gare shi daga ko'ina a duniya, Dukan kabilai za su yi masa sujada.


Ku nuna masa bangirma, ku kasa kunne ga maganarsa. Kada ku tayar masa, gama ba zai gafarta muku laifofinku ba, gama shi wakilina ne.


Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki, Ya ceci jama'arsa, Dukan duniya kuwa ta gani.


“Ku juyo wurina a cece ku, Ku mutane ko'ina a duniya! Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


“Da idanunku za ku ga wannan, za ku kuwa ce, Allah mai girma ne yake a ƙasar da ba ta Isra'ila ba ce!”


ni Ubangiji kuwa, zan kawo Sarkin Assuriya da dukan sojojinsa su fāɗa wa Yahuza. Za su tasar musu kamar rigyawar Kogin Yufiretis wadda ta yi ambaliya ta shafe kowace gaɓa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ