Ringin Yakubu kuma zai zamar wa al'umman duniya, Kamar yadda zaki yake a tsakanin namomin jeji, Kamar kuma yadda zaki yake a tsakanin garkunan tumaki, Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakan tattaka, Ya yi kacakaca da su, Ba wanda zai cece su.
Mutuwa ta ƙarfi da yaji za ku yi, gama sa'ad da na yi kiranku ba ku amsa ba, ba ku kasa kunne ba kuwa sa'ad da nake magana da ku. Kuka zaɓa ku yi mini rashin biyayya, ku kuma aikata mugunta.
Domin haka fa yanzu, sai ku kasa kunne ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah mai iko na Isra'ila, yake cewa, “Zan ɗauki fansa a kanku ku maƙiyana, ba za ku ƙara wahalshe ni ba.