Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mika 5:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Zan sassare siffofinku da ginshiƙanku, Ba za ku ƙara sunkuya wa aikin hannuwanku ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku, nan gaba ba za ku ƙara rusuna wa aikin hannuwanku ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mika 5:13
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗansunku da suka tsere za su tuna da ni cikin al'ummai inda aka kai su bautar talala yadda raina ya ɓaci saboda zuciyarsu ta rashin imani wadda ta rabu da ni, da idanunsu masu zina da suke bin gumaka. Za su kuwa ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwa da suka aikata.


Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.


A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.


Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka? Ni ne wanda yake amsa muku, mai lura da ku kuma. Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar. Daga gare ni, kuke samun 'ya'ya.”


Assuriya ba za ta cece mu ba, Ba kuwa za mu hau dawakai ba. Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu, ‘Kai ne Allahnmu,’ ba. A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”


Ba za su ƙara ƙazantar da kansu da gumaka da abubuwan banƙyama da kowane irin laifi ba. Zan komo da su daga riddar da suka yi, in tsarkake su. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu.


Ƙasarsu tana cike da gumaka, suna sujada ga abubuwan da suka yi da hannuwansu.


Sauran 'yan adam waɗanda bala'in nan bai kashe ba kuwa, ba su tuba sun rabu da abubuwan da suka yi da hannunsu ba, ba su kuma daina yin sujada ga aljannu, da gumakan zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na dutse, da na itace ba, waɗanda ba su iya gani, ko ji, ko tafiya,


Amma mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar suka shiga kai tsaye, suka ɗauki gunkin da aka yi da itace, da falmaran, da kan gida, da gunki na zubi. Firist ɗin kuwa ya tsaya a bakin ƙofa tare da mutum ɗari shida ɗin nan masu shirin yaƙi.


Zuciyarsu ta munafunci ce, Yanzu tilas za su ɗauki hakkin laifinsu, Ubangiji zai farfashe bagadansu da ginshiƙansu.


Ubangiji ya riga ya yi umarni a kanka cewa, “Sunanka ba zai ci gaba ba, Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofi Da siffofi na zubi daga gidan gumakanka. Zan shirya maka kabari, gama kai rainanne ne.”


“Zan miƙa hannuna gāba da Yahuza Da dukan mazaunan Urushalima. A wurin nan zan datse saura waɗanda suke bauta wa Ba'al, Da kuma sunayen firistocin gumaka tare da firistocina,


Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.


Za su kuma ƙone gidajenki, su hukunta ki a gaban mata da yawa. Ni kuwa zan sa ki bar karuwanci, ba za ki ƙara ba da kuɗi ga kwartayenki ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ