Domin haka hayaniyar yaƙi za ta tashi a tsakanin jama'arku. Dukan kagaranku za a hallaka su. Kamar yadda Shalmanesar ya hallaka Bet-arbel a ranar yaƙi. An fyaɗa uwaye da 'ya'yansu a ƙasa.
ka ce, ‘Zan haura, in tafi ƙasar da garuruwanta ba su da garu, in fāɗa wa mutanen da suke zama cikin salama, dukansu kuwa suna zaman lafiya, garuruwansu ba garu, ba su da ko ƙyamare,
Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?” Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.
Ya Allah, ka rabu da jama'arka, zuriyar Yakubu. Ƙasa ta cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas, daga kuma ƙasar Filistiya. Jama'a suna bin baƙin al'adu.
Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.