Mika 4:10 - Littafi Mai Tsarki10 Ki yi makyarkyata, ki yi nishi, ke Sihiyona, Kamar mace mai naƙuda, Gama yanzu za ki fita daga cikin birni, Ki zauna a karkara, Za ki tafi Babila, daga can za a cece ki. Daga can Ubangiji zai cece ki daga hannun maƙiyanki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona, kamar macen da take naƙuda, don yanzu dole ki bar birni ki kafa sansani a filin Allah. Za ki tafi Babilon; a can za a kuɓutar da ki. A can ne Ubangiji zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu, Don ya cika nufina ya daidaita al'amura. Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai. Zai sāke gina birnina, wato Urushalima, Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala. Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.” Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.