Mika 4:1 - Littafi Mai Tsarki1 Zai zama nan gaba, dutse inda Haikalin Ubangiji yake Zai zama shi ne mafi tsawo duka a cikin duwatsu, Zai fi tuddai tsayi, Mutane kuwa za su riƙa ɗunguma zuwa wurinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 A kwanakin ƙarshe za a kafa dutsen haikalin Ubangiji yă zama babba a cikin duwatsu. Za a ɗaga shi sama da tuddai, mutane kuma za su riƙa ɗunguma zuwa gare shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.
Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.