Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mika 3:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ga abin da Ubangiji ya ce a kan annabawan da suka bi da mutanensa a karkace, Waɗanda suke cewa, “Salama,” sa'ad da suke da abinci, Amma sukan kai yaƙin shahada Ga wanda bai ba su abin sawa a baka ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Game da annabawa masu ɓad da mutanena, in wani ya ciyar da su, sai su ce akwai ‘salama’ amma in bai ciyar da su ba, a shirye suke su kai masa hari.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mika 3:5
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sun warkar da raunin mutanena sama sama, Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya.


Ina kuma gāba da annabawan da suke annabcin mafarkansu na ƙarya, suna kuwa faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu, saboda rashin hankalinsu. Ni ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan jama'a ba ko kaɗan, ni Ubangiji na faɗa.”


Ai, irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Ubangijinmu Almasihu, sai dai cikinsu. Ta romon kunne da daɗin baki suke yaudarar masu sauƙin kai.


Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”


“Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.


“Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin hanci ce. Firistocinta suna koyarwa don neman riba, Haka kuma annabawa suna annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna dogara ga Ubangiji, suna cewa, “Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu, Ba masifar da za ta same mu.”


“Idan mutum ya tashi yana iskanci, yana faɗar ƙarya, ya ce, ‘Zan yi muku wa'azi game da ruwan inabi da abin sa maye,’ To, shi ne zai zama mai wa'azin mutanen nan!


Suna zaton za su sa mutanena su manta da sunana ta wurin mafarkansu da suke faɗa wa junansu, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana saboda Ba'al.


Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama'ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu. Ya jama'ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.


Ku sanar wa al'ummai da wannan, Su yi shirin yaƙi, Su kira mayaƙa! Su tattaro sojoji, su zo!


Nuna sonkai mugun abu ne, waɗansu alƙalai sukan aikata mugunta saboda 'yar ƙaramar rashawa.


Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa mata da yaƙi! Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakar rana!’ Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, ga rana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi.


Annabawanki sun gano miki wahayan ƙarya, Ba su tone asirin muguntarki, Har da za a komo da ke daga bauta ba. Amma suka yi miki annabcin ƙarya na banza.


Ikona zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya, waɗanda suke kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin mutanen Isra'ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani, ni ne Ubangiji Allah.


Za ku yi tuntuɓe da rana, Annabi kuma zai yi tuntuɓe tare da kai da dare, Ni kuwa zan hallaka mahaifiyarku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ