Mika 2:7 - Littafi Mai Tsarki7 Daidai ne a faɗi haka, ya jama'ar Yakubu? ‘Ruhun Ubangiji ya yi rashin haƙuri ne? Waɗannan ayyukansa ne?’ ” “Ashe, maganata ba takan amfana wanda yake tafiya daidai ba?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Daidai ne a ce, ya gidan Yaƙub, “Ruhun Ubangiji yana fushi ne? Yana yin irin waɗannan abubuwa?” “Ashe, maganata ba tă amfane wanda ayyukansa suke daidai ba? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Don me mutanena ba su amsa ba Sa'ad da na je wurinsu domin in cece su? Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu? Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne? Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina, Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada, Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.