Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mika 2:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ku tashi, ku tafi, Gama nan ba wurin hutawa ba ne, Saboda ƙazantarku wadda take kawo muguwar hallaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ku tafi, ku ba ni wuri! Gama wannan ba wurin hutunku ba ne, gama ya ƙazantu, ya zama kangon da ya wuce gyara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mika 2:10
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna.


Suka karkashe mutane marasa laifi, Wato 'ya'yansu mata da maza. Suka miƙa su hadaya ga gumakan Kan'ana, Suka ƙazantar da ƙasar saboda kashe-kashenkan da suke yi.


Gama haka Ubangiji ya ce, “Ga shi, ina jefar da mazaunan ƙasar daga ƙasarsu a wannan lokaci, Zan kawo musu wahala, za su kuwa ji jiki.”


“Gama ana jin muryar kuka daga Sihiyona cewa, ‘Ga yadda muka lalace! Aka kunyatar da mu ɗungum! Don mun bar ƙasar, domin sun rurrushe wuraren zamanmu.’ ”


Sai na ji haushi, na yi musu alkawari mai nauyi. Na ce, ‘Faufau ba za ku shiga ƙasar da zan ba ku hutawa a ciki ba.’ ”


to, sai in tumɓuke ka daga ƙasata wadda na ba ka, wannan Haikali kuma wanda na riga na keɓe domin sunana, zan kawar da shi daga fuskata, zan kuwa maishe shi abin karin magana, abin raini ga dukan sauran al'umma.


A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.


A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.


sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.


to, ina faɗa muku yau, lalle za ku hallaka. Ba za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun ku shiga ciki don ku mallake ta ba.


to, yau na kira sama da duniya su shaida a kanku, cewa lalle za ku hallaka nan da nan cikin ƙasar da za ku haye Urdun zuwa cikinta don ku mallake ta. Ba za ku daɗe cikinta ba, amma za a shafe ku ƙaƙaf.


Ki ta da idonki, ki duba filayen tuddai ki gani, Akwai wurin da ba ki laɓe kin yi karuwanci ba? Kin yi ta jiran abokan sha'anin karuwancinki a kan hanya, Kamar Balaraben da yake fako a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da mugun karuwancinki.


“Ɗan mutum, sa'ad da mutanen Isra'ila suka zauna a ƙasar kansu, sun ƙazantar da ita ta wurin hanyoyinsu da ayyukansu. Halinsu a gare ni ya zama kamar rashin tsarkin mace a lokacin hailarta.


Na warwatsa su cikin al'ummai, suka kuwa warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ