Mika 1:7 - Littafi Mai Tsarki7 Za a farfashe dukan siffofinta na zubi, Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta, Zan lalatar da gumakanta duka, Gama ta wurin karuwanci ta samo su, Ga karuwanci kuma za su koma.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.