Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 9:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Da taron suka ga haka, sai tsoro ya kama su, suka ɗaukaka Allah, wanda ya ba mutane iko haka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 9:8
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle, wani annabi mai girma ya bayyana a cikinmu,” da kuma, “Allah ya kula da jama'arsa.”


Har jama'ar suka yi ta al'ajabi da ganin bebaye suna magana, masu dungu sun sami gaɓoɓinsu, guragu na tafiya, makafi kuma suna gani, duk suka ɗaukaka Allah na Isra'ila.


Da kuma suka daɗa yi musu kashedi, suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama'a, domin dukan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku.


Sa'ad da jarumin ya ga abin da ya gudana, sai ya girmama Allah ya ce, “Hakika mutumin nan marar laifi ne!”


Ɗayansu kuma da ganin an warkar da shi, ya komo, yana ta ɗaukaka Allah da murya mai ƙarfi,


Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”


Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna 'ya'ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina.


Sai ya ɗora mata hannu, nan take ta miƙe, ta kuma ɗaukaka Allah.


Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al'ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”


Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan'uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari'a.


Suka yi mamaki gaba da kima, suka ce, “Kai, ya yi kome da kyau! Har kurma ma ya sa ya ji, bebe kuma ya yi magana.”


Sai Yesu ya matso, ya ce musu, “An mallaka mini dukkan iko a Sama da ƙasa.


Mutane duk suka yi al'ajabi, suka ce, “Shin, ko wannan shi ne Ɗan Dawuda?”


To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”


Makiyayan suka koma, suna ta ɗaukaka Allah, suna yabonsa, saboda duk abin da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.


Ashe, ba wanda aka samu ya komo ya ɗaukaka Allah, sai baƙon nan kaɗai?”


Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.


Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na'am da bisharar Almasihu, saboda kuma gudunmawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.


Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ