Wata rana da daddare aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya, ka taimake mu mana.”
Yasuwa kuma da ake kira Yustus yana gaishe ku. Wato, cikin abokan aikina ga Mulkin Allah, waɗannan su kaɗai ne daga cikin Yahudawa masu bi, sun kuwa sanyaya mini zuciya.