23 Da ya shiga jirgi, almajiransa suka bi shi.
23 Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.
Da ya shiga jirgi, ya haye ya je garinsu.
Sai ya amsa musu ya ce, “Ku je ku gaya wa Yahaya abin da kuka ji da abin da kuka gani. Makafi na samun gani, guragu na tafiya, ana tsarkake kutare, kurame na ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta bishara.
Sai ga wani babban hadiri ya taso a teku, har raƙuman ruwa suka fara shan kan jirgin, amma yana barci.
A ran nan da maraice ya ce musu, “mu haye can ƙetare.”