Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 8:12 - Littafi Mai Tsarki

12 'ya'yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 8:12
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”


Sa'ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon baki.


“Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.


su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”


su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.


yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon baki.”


Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.


Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.


Da yake Allah bai rangwanta wa mala'iku ba sa'ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci,


Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.


Ku ne tsatson annabawa, ku ne kuma magadan alkawarin da Allah ya yi wa kakanninku, da ya ce wa Ibrahim, ‘Ta zuriyarka ne za a yi wa dukkan kabilan duniya albarka.’


Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne.


“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.


Sa'ad da mugaye suka ga wannan, Sai suka tunzura, suka harare shi da fushi, suka ɓace, Sa zuciyarsu ta ƙare har abada.


Za su raira waƙa don farin ciki, amma ku za ku yi kuka da karayar zuci.


Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ