Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 7:6 - Littafi Mai Tsarki

6 “Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu'ulu'unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 7:6
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada ka yi wa wawa magana irin ta haziƙai, gama ba zai yaba da maganarka ba.


Wawan da yake maimaita aikin wautarsa yana kama da kare mai yin amai ya koma ya tanɗe.


Ku yi hankali da karnukan nan! Ku yi hankali da mugayen ma'aikatan nan! Ku yi hankali da masu yankan jikin nan!


Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.”


To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan?


Ai kuwa, karin maganar nan na gaskiya ya dace da su cewa, “Kare ya cinye amansa,” da kuma, “Gursunar da aka yi wa wanka ta kome ga birgima cikin laka.”


A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.


Kome kyan mace idan ba ta da kangado, tana kamar zoben zinariya a hancin alade.


sa'an nan kuma suka ridda, ba mai yiwuwa ba ne a sāke jawo su ga tuba, tun da yake sāke gicciye Ɗan Allah suke yi, su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari.


Na yi tafifiya da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin 'yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al'ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a bahar, na kuma sha hatsarin 'yan'uwa na ƙarya.


Idan ka amsa tambayar wauta, ka zama wawa daidai da mutumin da ya yi tambayar.


Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan'uwanka.


Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ