Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 7:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 7:2
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama Shari'a marar jinƙai ce ga wanda ba ya nuna jinƙai. Amma jinƙai yana rinjayar hukunci.


Sai ya ce musu, “Ku ji. Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a ƙara.


Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”


“Ranar da ni Ubangiji zan shara'anta al'ummai duka ta zo kusa, Ke, Edom, abin da kika yi, Shi ne za a yi miki. Ayyukanki za su koma a kanki.


Ku saka mata daidai da yadda ta yi, Ku biya ta ninkin ayyukanta, Ku dama mata biyun abin da ta dama muku.


Abin la'akari fa, shi ne wanda ya yi ƙwauron yafa iri, gonarsa za ta yi masa ƙwauron amfani, wanda kuwa ya yafa a yalwace, sai ya girba a yalwace.


Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.


Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona.


Sama'ila ya ce masa, “Kamar yadda takobinka ya mai da mata marasa 'ya'ya, haka za a mai da mahaifiyarka ta zama marar ɗa.” Sai Sama'ila ya sassare Agag gunduwa gunduwa a gaban bagade a Gilgal.


Yana jin daɗin la'antarwa, ka sa a la'anta shi! Ba ya son sa albarka, ka sa kada kowa ya sa masa albarka!


Magabtanmu sun shiga uku! Sun yi fashi sun ci amana, ko da yake ba wanda ya yi musu fashi ko cin amana. Amma lokacinsu na fashi da na cin amana zai ƙare, su ne kuma za a yi wa fashi da cin amana.


Domin haka ni Ubangiji na ce, ba biyayya kuka yi mini ba, da irin shelar 'yancin da kowannenku ya yi wa ɗan'uwansa da maƙwabcinsa, saboda haka ni zan yi muku shelar 'yanci zuwa mutuwa ta takobi, da annoba, da yunwa. Zan sa ku zama abin ƙyama ga dukan mulkokin duniya.


“Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku.


ido a maimakon ido, haƙori a maimakon haƙori, hannu a maimakon hannu, ƙafa a maimakon ƙafa,


Ya fāɗi a gwiwoyinta, Ya fāɗi ƙasa, yana kwance shiru a ƙafafunta. A ƙafafunta ya sunkuya ya fāɗi, Ya fāɗi matacce har ƙasa.


Suka ce wa sarki, “Mutumin da ya karkashe mu, ya yi niyyar hallakar da mu, don kada mu kasance tare da Isra'ilawa ko'ina a cikin karkararsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ