11 Ka ba mu abincinmu na yau.
11 Ka ba mu yau abincin yininmu.
Ka kawar da ƙarya nesa da ni. Kada ka ba ni talauci ko dukiya, sai dai ka ba ni abinci daidai da bukatata,
Ka ba mu abincin yau da na kullum.
Amma Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake cewa, “ ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba, Sai dai da kowace maganar da yake fitowa daga wurin Allah.’ ”
Har zakoki sukan rasa abinci su ji yunwa, Amma masu biyayya ga Ubangiji, Ba abu mai kyau da sukan rasa.
A kullum ina aikata abin da Allah ya umarta, Ina bin nufinsa, ba nufin kaina ba.
Sa'an nan za ku yi nasara, ku kuma zauna lafiya kamar kuna cikin kagara mai ƙarfi. Za ku sami abincin da za ku ci da ruwan da za ku sha.
To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.
To, irin waɗannan mutane muna yi musu umarni, muna kuma gargaɗinsu da izinin Ubangiji Yesu Almasihu, su riƙa aiki da natsuwa, suna ci da kansu.
Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta.