Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 5:39 - Littafi Mai Tsarki

39 Amma ni ina gaya muku, kada ku ƙi a cuce ku. Amma ko wani ya mare ka a kuncin dama, to, juya masa ɗayan kuma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

39 Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 5:39
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane.


Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.


Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako.


Bari ya yarda a mari kumatunsa, Ya haƙura da cin mutunci.


Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.


Kada ka ce, “Zan yi masa daidai da yadda ya yi mini, zan rama masa!”


Na tsiraita ga masu dūkana. Ban hana su sa'ad da suke zagina ba, Suna tsittsige gemuna, Suna tofa yau a fuskata.


Ku yi ƙarar juna ma, ai, hasara ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura a zambace ku?


Kun hukunta mai adalci, kun kuma kashe shi, bai kuwa yi muku tsayayya ba.


Mutane sun buɗe baki don su haɗiye ni Suna kewaye ni suna ta marina.


Famarku da zunubi ba ta kai har yadda za a kashe ku ba.


Suka ɗaure masa idanu, suka tambaye shi, suka ce, “Yi annabci! Wa ya buge ka?”


Sa'an nan Zadakiya ɗan Kena'ana ya matso kusa ya mari Mikaiya a fuska, ya ce, “Ƙaƙa Ruhun Ubangiji ya bar ni, ya zo ya yi magana da kai?”


Ki tattara sojojinki, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun Sarkin Isra'ila da sanda.


In kuwa wani ya yi ƙararka da niyyar karɓe taguwarka, to, ka bar masa mayafinka ma.


Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka yi haƙwansa su ga ko yā warkar a ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa.


Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu to, ka ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, don me za ka mare ni?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ