Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 4:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 4:19
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”


Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.


Ya kuma ce wa wani, “Bi ni.” Sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka bar ni tukuna in je in binne tsohona.”


Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!”


Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.”


Bayan haka ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.”


Yana cikin wucewa, sai ya ga Lawi ɗan Halfa a zaune yana aiki a wurin karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.


Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama kammalalle, sai ka je ka sayar da duk mallakarka, ka bai wa gajiyayyu, ka sami wadata a Sama. Sa'an nan ka zo ka bi ni.”


Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.


Amma Yesu ya ce masa, “Bi ni. Bari matattu su binne 'yan'uwansu matattu.”


To, a ce ban nauyaya muku ba ɗin, ashe, sai ku ce dabara na yi muku, na shawo kanku ta hanyar yaudara!


Yana tafiya a bakin Tekun Galili ke nan, sai ya ga waɗansu 'yan'uwa biyu, Saminu da ake kira Bitrus, da ɗan'uwansa Andarawas, suna jefa taru a teku, don su masunta ne.


Nan da nan, sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ