Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 3:6 - Littafi Mai Tsarki

6 yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 3:6
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da yawa kuma daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya suka zo, suna bayyana ayyukansu a fili.


In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.


tun da yake ci da sha da wankewanke iri iri kaɗai suke shafa, ka'idodi ne a game da jiki kurum, waɗanda aka sa kafin a daidaita al'amari.


“Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.


da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da ɗora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukunci.


An kuma binne ku tare da shi a wajen baftisma, inda kuma aka tashe ku tare da shi saboda bangaskiyarku ga ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.


Dukansu kuwa an yi musu baftisma ga bin Musa a cikin gajimaren, da kuma bahar ɗin.


To, a yanzu me kake jira? Tashi, a yi maka baftisma a wanke zunubanka ta wurin kira bisa sunansa.’ ”


Sai na tuna da Maganar Ubangiji, yadda ya ce, ‘Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma ku da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.’


domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin 'yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”


sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in ɓalle ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.


Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunabansu, yana yi musu baftisma a Kogin Urdun.


Na yi addu'a ga Ubangiji Allahna, na tuba. Na ce, “Ya Ubangiji, Allah maigirma, mai banrazana, kai mai cika alkawari ne, kana ƙaunar masu ƙaunarka waɗanda suke kiyaye dokokinka.


Zan yayyafa muku tsabtataccen ruwa, za ku kuwa tsarkaka daga dukan ƙazantarku, da kuma daga dukan gumakanku.


Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa'an nan Allah zai yi maka jinƙai.


Sa'an nan na hurta zunubaina gare ka, Ban ɓoye laifofina ba. Na ƙudurta in hurta su gare ka, Ka kuwa gafarta dukan laifofina.


Sai ya ce wa Akan, “Ɗana, ka ba da girma ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka yabe shi ka gaya mini abin da ka yi, kada ka ɓoye mini.”


sai ya hurta zunubinsa, sa'an nan ya biya cikakkiyar diyyar abin da ƙarin humushin abin, ya ba mutumin da ya yi wa laifin.


“Amma za su hurta muguntarsu da ta kakanninsu, da cin amana da suka yi mini, da kuma tayarwa da suka yi mini,


Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra'ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi.


Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu,


Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.


Sa'ad da Ezra yake yin addu'a, yana hurta laifi, yana kuka, yana a durƙushe gaban Haikalin Allah, sai babban taron jama'a, mata, da maza, da yara daga Isra'ila suka taru wurinsa. Mutane suka yi kuka mai zafi.


Zai kuma juyo da Isra'ilawa da yawa ga Ubangiji Allahnsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ