Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 27:54 - Littafi Mai Tsarki

54 Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

54 Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 27:54
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da jarumi ɗin da yake tsaye yana kallon Yesu, ya ga yadda ya mutu haka, sai ya ce, “Hakika mutumin nan Ɗan Allah ne!”


Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.”


Amma jarumin da ya so ya ceci Bulus, ya hana i da nufinsu, ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci,


Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu 'yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas.


Sa'an nan ya kira jarumi biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba'in, da 'yan māsu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.”


A nan tāke ya ɗibi soja da jarumawa, suka ruga zuwa wajensu. Su kuwa da ganin shugaban da soja suka daina dūkan Bulus.


Yana shiga Kafarnahum ke nan, sai wani jarumi ya zo gunsa ya roƙe shi,


Sai Mai Gwadawar nan ya zo, ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama gurasa.”


A nan tāke sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, sai ushirin garin ya zube, mutum dubu bakwai aka kashe a rawar ƙasar, sauran kuwa suka tsorata, suka ɗaukaka Allah Mai Sama.


amma ga tsarkinsa na ruhu shi Ɗan Allah ne, da iko aka ayyana shi haka ta wurin tashinsa daga matattu.


Bulus kuwa ya kira wani jarumi ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata magana da zai faɗa masa.”


An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.


To, da suka ji haka, maganar ta soke su a zuci, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “'Yan'uwa, me za mu yi?”


Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Sharian nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.”


Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.”


suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi a cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to sauko daga gicciyen mana!”


Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.”


Sai labulen da yake cikin Haikalin ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta yi girgiza, duwatsu kuma suka tsattsage.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ