44 Har 'yan fashin nan da aka gicciye su tare ma, su suka zazzage shi kamar waɗancan.
44 Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.
Almasihun nan, Sarkin Isra'ila, yă sauko mana daga gicciyen yanzu, mu kuwa mu gani mu ba da gaskiya.” Waɗanda aka gicciye tare da shi su ma suka zazzage shi.
Sai kuma aka gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a dama, ɗaya a hagun.
Sa'ad da nake shan wahala, Murna suke yi duka, Sun kewaye ni, suna ta yi mini dariya, Baƙi sun duke ni, suna ta buguna.
Gama ko Almasihu ma bai yi sonkai ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zagin da waɗansu suka yi maka duk yā komo kaina.”
In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.