36 Suka zauna a nan suna tsaronsa.
36 Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa.
Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”
Bilatus ya yi mamaki ko ya mutu. Sai ya kira jarumin ɗin, ya tambaye shi ko Yesu ya jima da mutuwa.
Sa'ad da jarumi ɗin da yake tsaye yana kallon Yesu, ya ga yadda ya mutu haka, sai ya ce, “Hakika mutumin nan Ɗan Allah ne!”
A daidai kansa aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.”