Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 27:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Da suka gama yi masa ba'a, sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufafi, suka tafi da shi su gicciye shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 27:31
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Aka ƙware shi ba tausayi, Amma ya karɓa da tawali'u, Bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya, Bai ko ce uffan ba.


Haka ma, Yesu ya sha wuya a waje bayan birni, domin yă tsarkake jama'a da nasa jini.


suka fitar da shi a bayan gari suka yi ta jifansa da dutse. Shaidu kuwa suka ajiye tufafinsu wurin wani saurayi, wai shi Shawulu.


Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi.


Sai suka fitar da shi daga cikin birni, suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.


A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, ‘Nabot ya zagi Allah da sarki.’ Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.”


Sa'an nan ya ce wa almajirin, “Ga tsohuwarka nan!” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.


Sa'an nan ya bāshe shi gare su su gicciye shi.


su bashe shi ga al'ummai, su yi masa ba'a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “A kashe mutumin, dukan taron jama'a za su jajjefe shi da duwatsu a bayan zangon.”


“Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”


Da suka gama yi masa ba'a haka, suka yaye masa alkyabba mai ruwan jar garura, suka sa masa nasa tufafi, suka kai shi waje don su gicciye shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ