Aka binne shi a kabarin da shi da kansa ya haƙa a birnin Dawuda. Aka sa shi a makara wadda aka cika da kayan ƙanshi da na turare yadda gwanayen aikin turare suka shirya, suka hura babbar wuta don su darajanta shi.
Sai Yusufu ya umarci barorinsa masu magani, su shafe gawar mahaifinsa da maganin hana ruɓa. Saboda haka masu maganin suka shafe Isra'ila da maganin hana ruɓa.