7 Duk 'yan matan nan suka tashi suka gyaggyara fitilunsu.
7 “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu.
“Ku yi ɗamara, fitilunku na kunne.
Saboda haka, ya ƙaunatattuna, tun da kuke jiran waɗannan abubuwa, ku himmantu ya same ku marasa tabo, marasa aibu, masu zaman salama.
Ka yi zaman tsaro, ka ƙarfafa abin nan da ya saura, yake kuma a bakin mutuwa, don ban ga aikinka cikakke ne ba a gaban Allahna.
“Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.
Can tsakar dare sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito ku tarye shi!’
Sai wawayen nan suka ce wa masu hikimar, ‘Ku sa mana ɗan manku kaɗan mana, fitilunmu na mutuwa!’