Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 25:45 - Littafi Mai Tsarki

45 Sa'an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

45 “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 25:45
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Idan ka ƙi jin kukan matalauci, naka kukan da kake yi na neman taimako, ba za a ji ba.


Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.


Shi kuma ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Sai ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.


Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’


Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.


Ya ce, “Kada ku taɓi bayina, zaɓaɓɓu, Kada ku cuci annabawana!”


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al'umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona.


Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki Sa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi. Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka, Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”


Waɗanda suka sa maka albarka zan sa musu albarka, amma zan la'anta waɗanda suka la'anta ka. Dukan al'umman duniya za su roƙe ni in sa musu albarka kamar yadda na sa maka.”


Wanda ya yi na'am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na'am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali.


Sa'an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?’


Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


Ta haka ne kuke yi wa Almasihu laifi, wato ta wurin yi wa 'yan'uwanku laifi, kuna rushe rarraunan lamirinsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ