Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 24:47 - Littafi Mai Tsarki

47 Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

47 Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 24:47
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’


Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’


Albarka tā tabbata ga bayin nan waɗanda ubangijinsu da zuwansa zai same su a faɗake. Hakika, ina gaya muku, zai yi ɗamara, ya ce su zauna cin abinci, sa'an nan ya bi ta kan kowannensu yana yi masa hidima.


Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallaka tasa.


Duk wanda ya ci nasara, zai ci wannan gādo, wato, in zama Allahnsa, shi kuma ya zama ɗa a gare ni.


Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.


In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi, In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,


Sai shi kuma ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki! Tun da ka yi gaskiya a kan ƙaramin abu, to, na ba ka mulkin gari goma.’


Sa'ad da kuma Sarkin Makiyaya ya bayyana, za ku sami kambin ɗaukaka marar dusashewa.


Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”


Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.


Sarakuna suna jin daɗin ƙwararrun 'yan majalisarsu, amma sukan hukunta waɗanda suka ba su kunya.


Albarka tā tabbata ga bawan da in ubangidansa ya dawo zai samu yana yin haka.


Amma in bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ