20 Ku yi addu'a kada gudunku ya zo da damuna, ko ran Asabar.
20 Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci.
Lura fa, Ubangiji ne ya ba ku ranar Asabar, domin haka a rana ta shida yakan ba ku abinci na kwana biyu. Kowanne ya yi zamansa a inda yake. Kada kowa ya bar inda yake a rana ta bakwai ɗin.”
Sai suka koma Urushalima daga dutsen nan da ake kira Dutsen Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima, wajen mil ɗaya.
Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!
A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.