Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 24:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 24:17
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Abin da nake gaya muku a asirce, ku faɗa a sarari. Abin da kuma kuka ji a raɗe, ku yi shelarsa daga kan soraye.


Kashegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu'a, wajen rana tsaka.


Don haka, kome kuka faɗa a asirce, za a ji shi a sarari. Abin kuma da kuka yi raɗa a loloki, za a yi shelarsa daga kan soraye


Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu.


“Saboda haka ina gaya muku, kada ku damu a kan rayuwarku game da abin da za ku ci, da abin da za ku sha, ko kuwa jikinku, abin da za ku yi sutura. Ashe, rai bai fi abinci ba? Jiki kuma bai fi tufafi ba?


Sa'ad da suka gangaro daga wurin yin sujadar zuwa cikin gari, sai aka shirya wa Saul gado a kan bene.


“Sa'ad da kuka gina sabon gida, sai ku ja masa rawani don kada ku jawo wa gidanku alhakin jini idan wani ya fāɗi daga bisa.


Shaiɗan ya amsa, ya ce, “Mutum ya iya rabuwa da dukan abin da yake da shi don yă ceci ransa.


Wata rana da yamma Dawuda ya tashi daga shaƙatawa, yana yawo a kan rufin soron fādarsa, can ya hangi wata kyakkyawar mata tana wanka.


to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.


Wanda yake a gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ