Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 23:38 - Littafi Mai Tsarki

38 Ga shi, an bar muku gidanku a yashe!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 Ga shi, an bar muku gidanku a yashe.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 23:38
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma idan ba ka kula da waɗannan zantuttuka ba, na rantse da zatina,’ in ji Ubangiji, ‘wannan fāda ta zama kufai.’ ”


Ga shi, an bar muku gidanku a yashe! ina kuwa gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”


Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”


“Sa'ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa'an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta.


“In don waɗannan abubuwa da kuke kallo ne, ai, lokaci yana zuwa da ba wani dutsen da za a bari a nan a kan ɗan'uwansa da ba a baje shi ba.”


sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.


“Sa'ad da kuka ga an kafa mummunan aikin saɓo mai banƙyama a wurin da bai kamata ba (mai karatu fa yă fahimta), to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.


Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa ba a baje shi ba.”


“Gama ba zan ƙara jin tausayin mazaunan ƙasan nan ba, ni Ubangiji na faɗa. Ga shi, zan sa su fāɗa a hannun junansu da a hannun sarkinsu. Za su lalatar da ƙasar, ba kuwa zan cece su daga hannunsu ba.”


Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara.


Ka kwarara musu fushinka, Bari zafin fushinka ya ci musu!


Allah ya sa su gudu su bar sansaninsu, Kada wani ya ragu da rai cikin alfarwansu!


Na ji Ubangiji Mai Runduna yana cewa, “Duk waɗannan manya manyan gidaje kyawawa za su zama kangwaye.


Ubangiji ya ce, “Na datse al'umman duniya, Hasumiyansu sun lalace. Na kuma lalatar da hanyoyinsu, Ba mai tafiya a kansu. An mai da biranensu kufai, Ba mutumin da yake zaune ciki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ