32 To, sai ku cikasa ayyukan kakanninku!
32 To, sai ku ci gaba ku cikasa ayyukan da kakanninku suka fara!
A tsara ta huɗu kuma, zuriyar za ta komo nan, domin adadin muguntar Amoriyawa bai cika ya kai iyaka ba tukuna.”
Ga shi, ku kuma da kuke 'ya'yan mugayen mutanen nan, ku da kuke a matsayin iyayenku, kuna so ku ƙara sa Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
suna hana mu yi wa al'ummai wa'azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.
Duk da haka ba su saurare ni ba, ba su kula su ji ba, sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.
Kakan nuna madawwamiyar ƙauna ga dubbai, amma kakan hukunta wa 'ya'ya saboda laifin ubanninsu. Ya maigirma Maɗaukaki, Allah, sunanka kuwa Ubangiji Mai Runduna.
“Za ka shara'anta su? Ɗan mutum, shara'anta su. To, sai ka sanar da su abubuwa masu banƙyama waɗanda kakanninsu suka yi.
Ta haka kuka shaidi kanku ku ne 'ya'yan masu kisan annabawa.
Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?