33 Da jama'a suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
33 Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
Sai dogaran suka amsa suka ce, “A'a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan!”
Duk suka yabe shi, suna mamakin maganarsa ta alheri da ya faɗa, har suka ce, “Ashe, wannan ba ɗan Yusufu ba ne?”
Duk waɗanda suka ji shi kuwa suka yi al'ajabin irin fahimtarsa da amsoshinsa.
Sai Yesu ya ce musu, “To, ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.” Sai suka yi mamakinsa ƙwarai.
Da Asabar ta yi, sai ya fara koyarwa a majami'a. Mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki, suna cewa, “Ina mutumin nan ya sami wannan abu duka? Wace hikima ce aka ba shi haka? Dubi irin waɗannan mu'ujizan da ake aikatawa ta hannunsa!
Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.