20 Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?”
20 sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”
“Ku nuna mini dinari. Surar wa da sunan wa yake a jikinsa?” Suka ce, “Na Kaisar ne.”
Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari.
Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”
Suka kawo masa. Ya ce musu, “Suran nan da sunan nan na wane ne?” Suka ce masa, “Na Kaisar ne.”