Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 21:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 21:1
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.


Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun.


Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.


Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?”


Sai suka koma Urushalima daga dutsen nan da ake kira Dutsen Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima, wajen mil ɗaya.


Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi.


Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.


Domin tausayi, sai Yesu ya taɓa idanunsu, nan take suka gani, suka bi shi.


ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure, da kuma ɗanta. Ku kwanto su.


Yana zaune a kan Dutsen Zaitun wanda yake kallon Haikalin sai Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, da Andarawas suka tambaye shi a keɓe suka ce.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ