32 Sai Yesu ya tsaya, ya yi kiransu ya ce, “Me kuke so in yi muku?”
32 Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”
Ubangiji Allah ya ce, “Ga abin da zan sa mutanen Isra'ila su roƙe ni, in yi musu. Za su roƙe ni in yawaita su kamar garken tumaki.
Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.
Sai ya ce mata, “Me kike bukata?” Ta ce masa, “Ka yi umarni waɗannan 'ya'yana biyu su zauna, ɗaya a damanka, ɗaya a hagunka, a mulkinka.”
Saboda haka da aka neme ni, na zo, ban ce a'a ba. To, yanzu ina so in ji abin da ya sa kuka kira ni.”
Jama'a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya suke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!”
Suka ce masa, “Ya Ubangiji, mu dai mu sami gani!”