Mattiyu 20:25 - Littafi Mai Tsarki25 Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani sarakunan al'ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202025 Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”