Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 19:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Sai ga wani ya matso wurinsa, ya ce, “Malam, wane aiki nagari ne da lalle zan yi in sami rai madawwami?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 19:16
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku tsaya a kan ƙaunar da Allah yake yi mana, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Almasihu mai kaiwa ga rai madawwami.


domin duk wanda ya gaskata da shi, ya sami rai madawwami.


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


wannan Rai kuwa an bayyana shi, mu kuwa mun gani, muna ba da shaida, muna kuma sanar da ku Rai madawwamin nan wanda tun dā yake tare da Uba, aka kuwa bayyana shi gare mu,


Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami.


Wannan shi ne alkawarin da ya yi mana, wato, rai madawwami.


duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil'azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,


Ta haka suke kafa wa kansu kyakkyawan tushe don nan gaba, domin su riƙi rai wanda yake na hakika.


Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa'ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa.


Sa'an nan ya fito da su waje, ya ce, “Ya shugabanni, me zan yi in sami ceto?”


Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da take bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.


Waɗanda suke neman daraja da ɗaukaka da kuma dawwama ta wurin naciyarsu ga aikata nagarta, zai saka musu da rai madawwami.


Mai ƙaunar ransa zai rasa shi. Wanda kuwa ya ƙi ransa a duniyan nan, ya kiyaye shi ke nan, har ya zuwa rai madawwami.


Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.


Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai kake da maganar rai madawwami.


Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.


Kuna ta nazarin Littattafai, don a tsammaninku a cikinsu za ku sami rai madawwami, alhali kuwa su ne suke shaidata.


Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.”


Kowa ya bar gidaje, ko 'yan'uwa mata, ko 'yan'uwa maza, ko uwa, ko uba, ko 'ya'ya, ko gonaki, saboda sunana, zai sami ninkinsu ɗari, ya kuma gāji rai madawwami.


Waɗanda suka rasu za su tashi, waɗansu zuwa rai madawwami, waɗansu kuwa zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci.


Duk da haka an yi mini jinƙai musamman, don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yă nuna cikakken haƙurinsa, in zama gurbi ga waɗanda a nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami.


Amma Yesu ya dube su, ya ce musu, “Ga mutane kam, ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ