Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 18:5 - Littafi Mai Tsarki

5 “Wanda duk ya karɓi ƙaramin yaro ɗaya kamar wannan saboda sunana, Ni ya karɓa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 18:5
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’


Ko da yake rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna mini raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na'am da ni kamar wani mala'ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa.


Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”


“Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”


Ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi ƙanƙane yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuwa ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ke nan. Ai, wanda yake ƙarami a cikinku shi ne babba.”


Kowa kuma ya ba ku ruwan sha moɗa guda saboda ku na Almasihu ne, hakika ina gaya muku, ba zai rasa ladansa ba ko kaɗan.


Sa'an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’


Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.


Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.


Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ