Da duk muka fāɗi, sai na ji wata murya tana ce mini da yahudanci, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Da wuya a gare ka ka yi ta shuri bisa a kan tsini.’
Don haka sai ya zo kusa da inda nake tsaye. Da ya zo sai na firgita, na faɗi rubda ciki. Amma ya ce mini, “Ɗan mutum, wannan wahayi yana a kan lokaci na ƙarshe ne.”
Wahayin da na gani ya yi kama da wahayin da na gani lokacin da ya hallaka birnin, kamar kuma wanda na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.
Dawuda ya ɗaga idonsa, sai ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsakanin sama da ƙasa, da takobinsa a zare a hannunsa a kan Urushalima. Sa'an nan Dawuda tare da dattawa suka fāɗi rubda ciki, suna saye da tufafin makoki.
Sa'ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala'ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa.
Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.
Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”