Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 17:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Duk da haka, don kada mu ba su haushi, ka je teku ka yi fatsa, kifin da ka fara kamawa kuwa shi za ka ɗauka. In ka buɗe bakinsa za ka sami shekel guda a ciki. To, sai ka ɗauki shekel ɗin nan ka kai musu, wato, nawa da naka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 17:27
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ba ma zamar wa kowa sanadin tuntuɓe, don kada a aibata aikinmu,


Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.


Sai dai ku lura, kada 'yancin nan naku ya zama abin sa tuntuɓe ga waɗanda ba su tsai da zuciyarsu ba.


Saboda haka in dai cin nama ya sa ɗan'uwana tuntuɓe, har abada ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa ɗan'uwana tuntuɓe.


Ubangiji kuwa ya umarci wani babban kifi ya haɗiye Yunusa. Yunusa kuwa ya yi yini uku da dare uku a cikin cikin kifin.


Da tsuntsaye da kifaye, Da dukan halittar da suke cikin tekuna.


Za ka riƙa samun ruwan sha daga rafin, na kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”


Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan'uwanku yin tuntuɓe.


Ubangiji kuwa ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gaɓar teku.


Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.”


Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe?


In idonka na dama yana sa ka yi laifi, to, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa duk jikinka ɗungum a Gidan Wuta.


In kuma hannunka na dama, yana sa ka yi laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓinka da a jefa jikinka ɗungum a Gidan Wuta.”


Sa'ad da kuma ya ce, “Daga wurin waɗansu,” sai Yesu ya ce masa, “Wato, 'ya'yan an ɗauke musu ke nan.


Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”


In kuwa hannunka ko ƙafarka suna sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai dungu ko da gurguntaka, da a jefa ka madawwamiyar wuta da hannu biyu ko ƙafa biyu.


“Da dai wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku.


In kuwa hannunka na sa ka laifi, to, yanke shi. Zai fiye maka ka shiga rai dungu, da ka shiga Gidan Wuta da hannu biyu, wuta marar kasuwa kuwa.


Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ