Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 16:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo suka roƙe shi ya nuna musu wata alama daga Sama, domin su gwada shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 16:1
33 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗansu kuwa, don su gwada shi, suka nema ya nuna musu wata alama daga Sama.


Suna cikin yin magana da jama'a sai firistoci da shugaban dogaran Haikali da Sadukiyawa suka ji haushi ƙwarai, suka aukar musu,


Sai Yesu ya ce musu, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”


Yahudawa kam, mu'ujiza suke nema su gani, Helenawa kuwa hikima suka nema su samu,


Sun faɗi haka ne don su gwada shi, ko sa sami hanyar kai ƙararsa. Amma Yesu ya sunkuya, ya yi ta rubutu a ƙasa da yatsa.


Amma babban firist ya taso, da duk waɗanda suke tare da shi, wato 'yan ɗariƙa Sadukiyawa, suna kishi gaya,


Sai waɗansu Sadukiyawa suka zo wurinsa (su da suke cewa, ba tashin matattu),


Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?”


Sai Sadukiyawa (su da suke cewa, wai ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka tambaye shi suka ce,


Mu biya, ko kada mu biya?” Shi kuwa da ya gane makircinsu, ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku kawo mini dinari in gani.”


Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wajensa don su gwada shi, suka tambaye shi suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa?”


Kashegari, wato, bayan ranar shiri, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka taru a gaban Bilatus,


“Malaman Attaura da Farisiyawa suka tsaya a matsayin Musa.


A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya,


Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai!


Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa.


Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa su gwada shi, suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa a kan kowane dalili?”


Waɗansu Farisiyawa da malaman Attaura suka zo wurin Yesu daga Urushalima, suka ce,


Amma Farisiyawa suka fita, suka yi shawara a kansa, yadda za su hallaka shi.


Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”


Ina dai gaya muku, in adalcinku bai fi na malaman Attaura da Farisiyawa ba, ba za ku shiga Mulkin Sama ba faufau.”


Ka amsa wauta ga tambayar wauta, wanda ya yi tambayar zai gane wawancinsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ