Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 14:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 14:9
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya ce musu, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, ‘Ka ga, yau ina fitar da aljannu, ina warkarwa, gobe ma haka, a rana ta uku kuwa zan gama aikina.


Sai sarki ya yi baƙin ciki gaya, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ba ya so ya hana ta.


don Hirudus yana tsoron Yahaya, ya sani shi mutum ne adali, tsattsarka, shi ya sa ya kāre shi. Hirudus yakan damu da yawa sa'ad da yake sauraron Yahaya, ko da yake na murna da jinsa.


Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


Ko da yake yana son kashe shi, yana jin tsoron jama'a, don sun ɗauka shi annabi ne.


A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu.


Yi tunani kafin ka yi magana, kada ka yi wa Allah wa'adi na gaggawa. Allah yana Sama kai kuwa kana duniya. Don haka kada ka faɗa fiye da abin da ya kamata.


Saul ya rantse mata da Ubangiji, ya ce, “Hakika, ba za a hukunta ki saboda wannan ba.”


Allah ya buge ni in mutu, idan na bar masa wani mutum da rai kafin gobe da safe.”


Sai wani daga cikin jama'a ya ce, “Ai, mahaifinka ya yi wa mutane barazana da rantsuwa cewa, ‘La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana.’ ” Mutane kuwa suka tafke.


A ran nan kuwa Isra'ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.


Mutanen Isra'ila kuwa suka yi wa Ubangiji ƙaƙƙarfan alkawari a Mizfa cewa, “Ba wani daga cikinmu da zai ba da 'yarsa aure ga mutumin Biliyaminu.”


Bayan wata biyu, sai ta koma wurin mahaifinta, shi kuwa ya yi abin da ya yi wa Ubangiji wa'adi. Ta rasu ba ta taɓa sanin namiji ba. Wannan kuwa ya zama al'ada a cikin Isra'ila,


Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, ‘Ku da matanku kun faɗa da bakinku, kun kuma aikata da hannuwanku, cewa za ku aikata wa'adodin da kuka yi na ƙona turare, da miƙa hadayu na sha ga sarauniyar sama.’ To, sai ku tabbatar da wa'adodinku, ku cika su!


Amma da uwa tasa ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi yanzu yanzu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ