25 Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tekun.
25 Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.
Ba wanda ya taimaki Allah shimfiɗa sammai, Wanda yake taka raƙuman ruwan teku, ya kuma kwantar da su.
Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko huɗu, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan ruwan, ya kusato jirgin. Sai suka firgita.
da ya ga suna fama da tuƙi, gama iska na gāba da su, misalin ƙarfe uku na dare sai ya nufo su, yana tafe a kan ruwan teku. Ya yi kamar zai wuce su,
Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.
In kuwa ya zo da tsakar dare ne, ko kuwa bayan tsakar dare, ya same su a faɗake, bayin nan masu albarka ne.
Ka gina wurin zamanka a bisa kan ruwan da yake sama. Gajimare ne karusanka, A bisa kan fikafikan iska kake tafiya.
Sai mala'ikan nan da na gani a tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama,
Ga wani ƙaramin littafi a buɗe a hannunsa. Sai ya tsai da ƙafarsa ta dama a kan teku, ƙafarsa ta hagu kuwa a kan ƙasa,
Sa'an nan muryar nan da na ji daga sama ta sāke yi mini magana, ta ce, “Je ka, ka ɗauki littafin nan da yake a buɗe a hannun mala'ikan da yake a tsaye a bisa teku da ƙasa.”
To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne,