Mattiyu 13:57 - Littafi Mai Tsarki57 Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202057 Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.