1 A ran nan Yesu ya fita daga gidan, ya je ya zauna a bakin teku.
1 A ranan nan sai Yesu ya fita daga gida ya je ya zauna a bakin tafkin.
Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawa a gonar.”
Da ya shiga wani gida sai makafin suka zo gare shi. Yesu ya ce musu, “Kun gaskata ina da ikon yin haka?” Sai suka ce masa, “I, ya Ubangiji!”
Yesu ya sāke fita bakin teku. Duk jama'a suka yi ta zuwa wurinsa, yana koya musu.
Ai, kowa ya yi abin da Ubana da yake cikin Sama yake so, shi ne ɗan'uwana, shi ne 'yar'uwata, shi ne kuma tsohuwata.”