Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 12:26 - Littafi Mai Tsarki

26 In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, yā rabu a kan gāba ke nan. To, ta yaya mulkinsa zai ɗore?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 12:26
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,


Mun sani mu na Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.


Mala'ika na biyar ya juye abin da yake a tasarsa a kursiyin dabbar nan, sai mulkinta ya zama duhu, har mutane suka ciji leɓunansu don azaba,


Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.


Sarkinsu kuwa da yake iko da su shi ne mala'ikan mahallaka, sunansa da Yahudanci Abadan, da Helenanci kuwa Afoliyon.


Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.


a kan hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulkin duniyar nan hukunci.


Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina,


Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan.


Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa, ‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Amma sai Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljannu yake fitar da aljannu.”


Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ