Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 11:14 - Littafi Mai Tsarki

14 In kuma za ku karɓa, shi ne Iliya da dā ma zai zo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 11:14
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ga shi, zan aiko muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji ta zo.


Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya. Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu, Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai, Ya tanada wa Ubangiji jama'a, ya same su a shirye.”


Nono ne na shayar da ku, ba abinci mai tauri na ba ku ba, don ba ku isa ci ba a lokacin, ko a yanzu ma ba ku isa ba,


“Ina da sauran abubuwa da yawa da zan gaya muku tukuna, amma ba za ku iya ɗaukarsu a yanzu ba.


Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.


Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.


A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”


Domin dukan annabawa da Attaura sun yi annabci har ya zuwa kan Yahaya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ