Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mattiyu 10:32 - Littafi Mai Tsarki

32 “Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mattiyu 10:32
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk wanda ya ci nasara, za a sa masa fararen tufafi, ba kuwa zan soke sunansa daga Littafin Rai ba, zan ce shi nawa ne a gaban Ubana, da kuma a gaban mala'ikunsa.


Kowa ya bayyana yarda, cewa Yesu Ɗan Allah ne, sai Allah yă dawwama a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.


Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah,


“ ‘Na san a inda kake da zama, wato, a inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kuwa, ka tsaya a gare ni, ba ka bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, a inda Shaiɗan yake zaune.


Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Iyayensa sun faɗi haka ne don tsoron Yahudawa, don dā ma Yahudawa sun ƙulla, cewa kowa ya amsa, cewa shi ne Almasihu, za a fisshe shi daga jama'a.


Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.


Zan hurta umarnanka ga sarakuna, Ba kuwa zan ji kunya ba.


Haka nake gaya muku, abin farin ciki ne ga mala'ikun Allah in mai zunubi guda ya tuba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ